Daga BELLO A. BABAJI
Mai Shari’a Maryanne ta Babbar Kotun Tarayya ta yi watsi da batun neman belin tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
Alƙalin ta yi hakan ne saboda a lokacin da aka rubuta takardar belin, tsohon gwamnan ba ya hannun Hukumar EFCC, wadda ita ta maka shi kotu.
A ranar 22 ga Nuwamba ne aka shigar da takardar yayin da aka kai Yahaya Bello ofishin EFCC a ranar 26 ga watan kuma aka gurfanar da shi a ranar 27.
Sauran bayanai za su zo daga baya…..