Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta tsawaita wa’adin tsoffin kuɗi zuwa Disamba

Daga BASHIR ISAH

Kotun Ƙoli ta ba da umarnin a ci gaba da amfani da tsoffin takardun N200 da N500 da kuma N1000 har zuwa 31 ga Disamban 2023.

Kotun ta ce tsoffin kuɗin za su ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da sabbin da aka samar.

A ranar Juma’a, Kotun, ƙarƙashin jagorancin Alƙali Inyang Okoro ta ba da wannan umarni inda ta ce umarnin sauya Naira 200, 500 da 1000 da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bai wa Babban Bankin Ƙasa (CBN) ba tare da ya tuntuɓi jihohi da Majalisar Zartarwa da Majalisar Tsoffin Shugabannin Ƙasa ba, hakan ya saɓa wa doka.

Kotun ta ce ta lura babu wata muhimmiyar sanarwar da aka bayar kafin aiwatar da tsarin kamar yadd Dokar CBN ta tanada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *