Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta sauke Gwamnan Filato

Daga BASHIR ISAH

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke Caleb Muftwang na PDP a matsayin halastaccen zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Filato sannan ta ayyana Dr Nentawe na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓe.

Kotun ta yanke hukuncin ne a zaman da ta yi a wannan Lahadin.

Alƙalan kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Williams-Dawodu, sun ayyana ɗan takarar Jam’iyyar APC, Dr. Nentawe Yilwatda, a matsayin halastaccen wanɗa ya lashe zaɓen.

Kotun ta umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), da ta janye shahadar lashe zaɓen da ta miƙa wa Mutfwang sannan ta miƙa wa Dr. Yilwatda.