Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Laraba ne Majalisar Dattijai ta tabbatar da Bianca Odumegu-Ojukwu a matsayin sabuwar ƙaramar Ministar Harkokin Waje.
Sauran ministocin sun haɗa da; Dakta Jumoke Oduwole a matsayin Ministar Masana’antu da Kasuwanci da Ci-gaba, da Nentawe Yilwatda a matsayin Ministan Jin-ƙai da Rage Talauci da kuma Muhammadu Dingyaɗi a matsayin Ministan Ƙwadago da Ɗaukar aiki.
Haka nan, ta kuma tabbatar da Idi Muktar a matsayin Ministan Ci-gaban Kiwo, sai Yusuf Ata wanda shi ne sabon Ministan Gine-gine da kuma Dakta Suwaiba Sa’id Ahmad a matsayin ƙaramar Ministar Ilimi.
Sauran bayanai za su O daga baya…