Daga BELLO A. BABAJI
Majalisar Dattawa ta bada umarnin kamo Darakta-Manaja na kamfanin Julius Berger, Dakta Peter Lubasch saboda ƙin amince wa haɗuwa da kwamitinta na ayyuka.
Majalisar ta yi hukuncin ne a lokacin da Mai tsawatarwa na ɓangaren marasa rinjaye, Sanata Osita Ngwu (PDP Enugu ta Yamma) ya shigar da batun.
Batun, wanda Sanata Asuquo Ekpenyong da Mpigi Barinada suka ɗauki nauyinsa, ya sanar da Majalisar cewa Manajan Kamfanin ya ƙi amince wa bayyana a gaban kwamitin ne wanda ke neman ya bada bayanai game da ayyukan da aka jingine waɗanda kuɗinsu ya kai N54bn zuwa N195bn.
Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya ce za a rubuta ranar da za a tilasta wa kamfanin zuwa gaban kwamitin a takardar umarnin kamawar.