Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar Dokokin Jihar Legas ta dakatar da zamanta har illa masha Allah

Daga BELLO A. BABAJI

Majalisar Dokokin Jihar Legas ta dakatar da zaman da ta saba yi a zaurenta, biyo bayan samame da jami’an ƴan sandan farin kaya, wato DSS suka kai mata a ranar Litinin.

Blueprint ta ruwaito cewa, jami’an sun rufe ofishin Kakakinta da na mataimakinta gabannin fara zama a ranar.

A yayin zaman ne ƴan majalisar suka bayyana aikin jami’an a matsayin saɓa wa dokar aiki tare da jaddada goyon baya ga Kakakin Majalisar, Mojisola Meranda.