Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar Wakilai ta amince da dokar ta-ɓaci a Ribas

Daga BELLO A. BABAJI

Duk da cewa an samu wasu da suka nuna rashin goyon bayansu ga hukuncin, Majalisar Wakilai ta amince da sanya dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas da Shugaba Bola Tinubu ya yi.

A ranar Talata ne Shugaban ƙasar ya sanar da sanya dokar, biyo bayan ƙamari da rikicin siyasar jihar ya yi, inda ya dakatar da gwamnan jihar da mataimakiyarsa da kuma ɗaukacin mambobin Majalisar Dokoki ta jihar.

Kakakin Majalisar, Tajuddeen Abbas ya bayyana cewa duk da cewa wasu na ganin batun bai samu adadin mutanen da ake buƙata ba, ya ce mambobi 243 ne suka halarci zaman, inda a dokance 240 sun wakilci kaso biyu bisa uku na adadin ƴaƴan majalisar 360 da ake da su.

Majalisar ta nemi a kafa kwamiti da zai warware matsalolin rikicin da dawo da zaman lafiya a jihar.

Abu na biyu, Majalisar Wakilan ta na son ta karɓi ragamar jagorancin Majalisar Dokoki ta jihar na tsawon watanni shida.