
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Litinin ne aka samu wani wasan kwaikwayo a Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, inda lauyan Nnamdi Kanu, Aloy Ejimakor ya faɗa wa Mai Shari’a Binta Nyako cewa ta tsame hannunta a shari’ar wanda ya ke karewa.
Saidai Mai Shari’ar ta mayar da martani da cewa Babban Alƙali bai amince da ta cire hannu a shari’ar ba, wanda ya sake mayar mata da ƙarar a ƙarƙashin ikonta.
Ta faɗa wa tawagar masu kare wanda aka shigar ƙarar ƙarƙarshin jagorancin Ejimakor cewa su aiko a rubuce matuƙar suka nace akan sai ta cire hannu a shari’ar.
Daga nan ne sai aka ɗage sauraron ƙarar zuwa wani lokaci da ba a bayyana ba.
Kanu ya halarci harabar kotun ne tare da jami’an DSS da misalin ƙarfe 8 na safe.
Tun a shekarar 2021 ne aka tsare Kanu bisa laifin ta’addanci da cin amanar ƙasa a yayin fafutukar Biafra inda aka maka shi kotu a ƙarƙashin hukuncin Mai Shari’a Binta Nyako.