Da ɗumi-ɗumi: Sanatan APC, Ali Ndume ya yi rashin Mahaifi

Daga AMINA YUSUF ALI

Mahaifin ɗaya daga cikin sanatocin Jam’iyyar APC mai wakiltar gundumar Kudancin Borno a Majalisar Dattawa ta Nijeriya, Sanata Mohammed Ali Ndume, ya riga mu gidan gaskiya.

Wannan sanarwar ta rashin mahaifin sanatan tana ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da Sanatan ya yi ranar Talata, 19 ga watan Yuli, 2022 a Abuja.

Ɗan majalisar ya bayyana cewa, za a yi jana’izar mahaifin nasa ne Alhaji Ali Buba Ndume, a ranar Talata a garin Maiduguri babban birnin Jihar Borno.

Wani sashen na sanarwar ya yi bayani kamar haka: “Muna masu nadamar sanar da rasuwar Alhaji Ali Buba Ndume, mahaifin Sanata Mohammed Ali Ndume. Ya rasu ne a safiyar yau Talata a garin Maiduguri”.

“Muna roqon Allah Subhanahu wa Ta’alah ya yafe masa kura-kuransa kuma ya ba iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi”.

Rahotanni sun bayyana cewa, an yi jana’izar Marigayin ne ƙarfe huɗu na yamma a gidansa da ke unguwar Damboa road kusa da ofishin tashar Talabijin ta NTA a birnin Maiduguri.

Da ma dai a farkon makon nan Majalisar Dattawa ta ɗage zamanta na ranar Talata zuwa Laraba domin nuna alhini ga rasuwar ɗaya daga cikin mambobinta na majalisar wakilai Jude Ise-Idehen, wanda ya mutu a kwanakin baya.