Da Ɗumi-ɗumi: Saudiyya ta ga watan Ƙaramar Sallah

Daga BASHIR ISAH

Kwamitin Duban Wata na Ƙasar Saudiyya, ya tabbatar da ganin watan Sallah Ƙarama (Shawwal) a yankin Sudair.

Shugaban Kwamitin, Dr. Abdullah Khudairi, shi ne ya sanar da hakan, inda ya ce sun ga watan Shawwal na shekarar 1444 da yammacin Alhamis a Sudair.

Da wannan ya tabbata watan Ramadan zai tiƙe ne a 29 a ƙasar, sannan wahse gari Juma’a ta kasance 1 ga Shawwal wanda ya yi daidai da 21 ga Afrilu, 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *