
Daga BELLO A. BABAJI
Sanannen jagoran ƙungiyar kabilar Yoruba ta Afenifere, Pa Ayo Adebanjo ya rasu bayan shafe shekaru 96 a duniya.
Iyalansa suka bayyana hakan a wata takarda da suka aika wa manema labarai a ranar Juma’a, 14 ga watan Fabrairu,
Takardar, wadda ke ɗauke da sanya hannun wasu daga cikin iyalan nasa da suka haɗa da Misis Ayotunde Atteh (nee Ayo-Adebanjo), Misis Adeola Azeez (nee Ayo-Adebanjo), da kuma Mista Obafemi Ayo-Adebanjo ta ce marigayin ya rasu ne a gidansa dake Lekki a Jihar Legas.
Adebanjo tsohon lauya ne kuma Sakataren shirye-shirye na jam’iyyar Action Group, sannan kuma ɗaya daga cikin manyan ƙasa.
Ya rayu ne tare da matarsa mai shekaru 94, Cif Christy Ayo-Adebanjo da ƴaƴa da jikoki da kuma tattaɓa-kunni.
Sanarwar ta ƙara da cewa, za a cigaba da tunawa da shi kan yaƙin neman gaskiya da adalci da ci-gaban Nijeriya.