Daga BASHIR ISAH
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bar Legas zuwa Abuja a ranar Lahadi bayan kammala hutun bikin Babbar Sallah na kwana huɗu.
Idan za a iya tumawa, a ranar Talatar da ta gabata Tinubu ya sauka Nijeya daga London bayan kammala babban taro da ya halarta a ƙasa Faransa.