Da Ɗumi-ɗumi: Shugaban Majalisar Ekiti, Hon. Funminiyi Afuye ya kwanta dama

Daga BASHIR ISAH

Wata majiya mai tushe daga Jam’iyyar APC na Jihar Ekiti ya shaida wa jaridar New Telegraph cewa: “Mun rasa Shugaban Majalisar Jihar Ekiti sakamakon bugun zuciya.”

Haka nan, Gwamnatin Jihar Ekiti ta ba da sanarwar rasuwar Shugaban Majalisar cikin sanarwar da ta fitar ta hannun Sakataren Yaɗa Labarai ga Gwamnan Jihar, Mr. Yinka Oyebode.

Sanarwar ta ce Afuye ya rasu ne da yammacin Laraba a Asibitin Koyarwa na Jihar (EKSUTH),  da ke Ado-Ekiti babban birnin jihar sakamakon fama da bugun zuciya.

Marigayin ya bar duniya yana da shekara 66. Kafin rsuwarsa, tsohon Kwamishina ne a Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta jihar, kuma sau biyu yana zama mamba a Majalisar Dokokin jihar inda ya wakilci mazaɓar Ikere ta ɗaya.

Bayanai sun ce ko a Lahadin da ta gabata, an ga Afuye a wajen bikin rantsar da Gwamna Biodun Oyebanji na jihar, kuma ya halarci zaman majalisa a Talatar da ta gabata.