Da ɗumi-ɗumi: Sojoji sun daƙile yinƙurin hare-haren ISWAP

Sojojin Nijeriya na ƙasa da sama sun yi nasarar daƙile yinƙurin kai harin mayaƙan ISWAP da suka mamaye yankin Buni Yadi a jihar Yobe

Duk da nasarar da sojojin suka samu a kan mayaƙan na ISWAP, tun farko sai da mayaƙan suka banka wa wani ofishin ‘yan sanda wuta kafin daga bisani sojoji suka katse musu hanzari.

Bayanan sojojin sun nuna mayaƙan sun tsere don neman mafaka sakamakon luguden wutar da suka sha a wajen sojojon.

An ce an ga jiragen yaƙin sojojin sama ƙirar Super Tucano na shawagi a yankin tabkin Chadi tare da yin luguden wuta a kan mayaƙan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *