Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya dakatar da shugaban EFCC, Bawa

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya dakatar da Shugaban Hukumar EFCC, AbdulRasheed Bawa, har baba-ta-gani.

An dakatar da Bawa ne domin samun damar gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi masa na yin amfani da ofishinsa wajen aikata ba daidai ba.

Sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey, ya fitar ta ce, an dakatar da Bawa ne saboda zargin da ake yi masa na keta alfarmar ofishinsa.

“An umarci Bawa da ya gaggauta miƙa ragamar ofishinsa ga Daranktan Ayyuka a hukumar, wanda shi zai ci gaba da kula da hukumar zuwa lokacin da za a kammala bincike,” in ji sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *