Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya koma Landan domin hutun shekara

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na shirin tafiya ƙasar Ingila domin hutun shekara.

Tinubu dai ya tafi ƙasar Birtaniya ne bayan tafiyarsa ƙasar Sin a watan Satumba.

Wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman Bayo Onanuga ya fitar a ranar Laraba, ya ce zai yi amfani da makonni biyu a matsayin hutun aiki, da kuma ja da baya don yin tunani kan sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatinsa.

Zai dawo ƙasar ne bayan kammala hutun.

Shugaban ƙasar in bamu mance ba ya yi bikin cikar Nijeriya shekaru 64 da samun ‘yancin kai da jawabi ga ‘yan ƙasa inda ya ce gwamnatin tarayya za ta gabatar da wani shiri na tsawon kwanaki 30 da nufin shigar da matasa cikin gwamnati.