Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya miƙa wa Majalisa sunayen ministoci kashi na biyu

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya miƙa wa Majalisar Tarayya sunayen ministocinsa kashi na biyu don tantancewa.

Tinubu ya miƙa sunayen ne ta hannun Shugaban Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila a ranar Laraba.

Manhaja ta tattaro cewar sunayen sun shafi jihohin Adamawa, Bayelsa, Gombe, Kano, Kebbi, Kogi, Lagos, Plateau, Osun, Yobe da kuma Zamfara.

Idan za a iya tunawa a ranar Alhamis ta makon jiya Gbajabiamila ya miƙa kashin farko sunayen mutum 28 ga Majalisar Dattawa domin tantace su a matsayin ministoci.

Ƙarin bayani na tafe…..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *