Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya naɗa Yemi Cardoso Gwamnan CBN

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da a naɗa Dr. Olayemi Michael Cardoso a matsayin sabon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), na wa’adin shekara biyar ya zuwa lokacin Majalisar Dattawa za ta tabbatar da naɗin nasa.

Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da ta fito ta bakin mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce naɗin ya yi daidai da Sashe na 8 (1) na Dokar Babban Bankin Nijeriya na 2007, wanda ya sahale wa Shugaban Ƙasa ikon naɗa Gwamnan CBN da mataimaka huɗu gabanin Majalisar Tarayya ta tabbatar da naɗinsu.

Kazalika, Bola Tinubu ya amince da a naɗa sabbin mataimakan Gwamnan CBN huɗu na wa’adin shekara biyar kafin Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗinsu nan gaba.

Sabbin mataimakan Gwamnan CBN ɗin su ne:

(1) Mrs. Emem Nnana Usoro

(2) Mr. Muhammad Sani Abdullahi Dattijo

(3) Mr. Philip Ikeazor

(4) Dr. Bala M. Bello

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *