Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya rattaɓa hannu kan Dokar Bai wa Ɗalibai Rancen Karatu

Daga BASHIR ISAH

A ranar Laraba Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya rataɓɓa hannu kan Dokar Bai wa Ɗalibai Rancen Karatu ta 2024.

Da wannan, sabuwar dokar za ta fara aiki ke nan, inda za ta bai wa ɗalibai a manyan makarantu zarafin samun rance daga gwamnati domin gudanar da harkokin karatunsu.

Tinubu ya sanya wa dokar hannu ne bayan da Majalisar Tarayya ta nazarci rahoton Kwamitin Kula da Manyan Makarantu da kuma asusun TETFund.