Daga BELLO A. BABAJI
Ɗan takarar jam’iyyar Republican a zaɓen Amurka, Donald Trump ya kere matakin adadin ƙuri’un masu zaɓe na 270 da ake so ɗan takarar ya samu wajen lashe zaɓen 2024.
Trump ya doke abokiyar ƙarawarsa ta jam’iyyar Democrats, Kamala Harris ne bayan samun ƙuri’un zaɓe 277 wanda hakan ya ba shi damar samun gurbin zama shugaban ƙasar na 47.
Ɗan takarar na Republican ya samu yin nasara a manyan jihohi da suka haɗa da; Arewacin Carolina, Georgia, Pennsylvania da Wisconsin.
Sauran sune; Indiana, Kentucky, Yammacin Virginia, Florida, Tennessee, Kudancin Carolina, Oklahoma, Mississippi, Alabama, Texas, Iowa da dai sauransu.
A shekarar 2016 ne aka fara zaɓen Trump a matsayin shugaban ƙasar inda ya doke Sakatariyar gwamnatin ƙasar ta wancan lokaci, Hillary Clinton.