Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro takwas a Imo

Bayanan da muka samu daga Jihar Imo na nuni da cewa ‘yan bindiga sun kashe jami’an tsaro takwas a jihar a ranar Talata.

Jaridar News Point Nigeria ta rawaito cewa, waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da sojoji da ‘yan sanda da jami’an sibul difens.

Majiyar tamu ta ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Umualumaku da ke yankin Ƙaramar Hukumar Ehime Mbano a jihar.

Ta ce ‘yan bindigar sun yi wa jami’an kwanton ɓauna ne a cikin motocinsu inda suka buɗe musu wuta kana daga bisani suka banka musu wuta.

Majiyar ta ƙara da cewa babu ko mutum guda da ya tsira daga jami’an tsaron.

Da aka nemi jin ta bakinsa, mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar, Henry Okoye, ya tabbatar wa News Point Nigeria da faruwar hakan, amma cewa yana buƙatar lokaci don fitar da cikakken rahoto kan batun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *