Da ɗumi-ɗumi: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 23 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Aƙalla mutane 23 da suka haɗa da mata biyu da ’ya’yan tsohon akawun jihar Zamfara, Alh. Abubakar Bello, wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a garin Furfuri da ke ƙaramar hukumar Bunguɗu a jihar ta Zamfara.

Wani mazaunin yankin mai suna Malam Haruna Manaja Furfuri a wata tattaunawa ta wayar tarho da Blueprint Manhaja, ya ce ‘yan bindigar sun yi wa garin ƙawanya ne da misalin ƙarfe 2:30 na safiyar Litinin.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun je kai tsaye gidan tsohon Akanta-Janar na Zamfara, Alh. Abubakar Bello, inda suka yi garkuwa da matansa guda biyu da ‘ya’yansa uku a lokacin harin.

Malam Haruna Manaja ya ƙara da cewa, matan biyu da aka yi garkuwa da su da sauran wasu mata sun kuɓuta ne sa’o’i kaɗan bayan da aka yi garkuwa da su.

“Bayan da al’ummar yankin suka bi sawun ɓarayin cikin daji, sai ‘yan bindigar suka bar waɗanda aka sace suka gudu, haka dai wasu daga cikin waɗanda aka sace ciki har da mata biyu na Alh. Abubakar Bello suka samu nasarar tserewa,” inji shi.

Ya ce har yanzu ‘ya’yan tsohon Akanta-Janar ɗin su uku har da wata budurwa da za a aurar da ita, har yanzu suna hannun ‘yan bindigar.

“Kamar yadda nake magana da kai yanzu, ‘yan ta’addar sun yi magana ta wayar tarho inda suka buƙaci kuɗi daga hannun tsohon Akanta-Janar ɗin a matsayin kuɗin fansa kafin su sako ‘ya’yan nashi su uku dake a hannun su”.

A halin da ake ciki kuma, Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara, SP. Muhammad Shehu, a wata hira da Blueprint Manhaja, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Shehu ya bayyana cewa rundunar ‘Yan sandan tana ƙoƙarin ganin an ceto waɗanda aka yi garkuwa da su lafiya.

Ya ce, “Tuni an tura tawagar bincike da ceto a maɓuyar ‘yan ta’addar don tabbatar da cewa an kuɓutar da waɗanda ke hannunsu lafiya.”