Da ɗumi-ɗumi: ‘Yan sanda sun cafke ɗan majalisa ɗauke da $500,000 a Ribas

Daga WAKILINMU

‘Yan sanda a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas, sun cafke ɗan Majalisar Wakilai, Hon. Chinyere Igwe, da safiyar Juma’a ɗauke da kuɗi sama da Dala dubu 500 ($500,000.00), yayin da ya rage sa’o’i 24 kafin zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan majalisar tarayya a Nijeriya.

Binciken Blueprint Manhaja ya gano cewa, kuɗin da aka kama Igwe da shi ana zargin ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ne ya ba shi tare da wata takarda mai ɗauke da sunayen ƙananan hukumomi 23 na jihar da hukumomin tsaro da kuma Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC).

Sai dai ya zuwa haɗa wannan labari, rundunar ‘yan sandan jihar ba ta ce komai ba tukuna a kan batun.

Ƙarin bayani na tafe…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *