Da ɗumi-ɗumi: ‘Yan sandan Kano sun garƙame ofishin lauyan Shekarau bayan kayar da Ganduje a kotu

Daga WAKILINMU

Rahotanni daga jihar Kano sun nuna cewa, jami’an Ma’aikatar Filaye ta Jihar tare da haɗin gwiwar ‘yan sanda sun garƙame ofishin lauyan Sanata Shekarau, Nureini Jimoh, SAN, da ke lamba 16c kan titin Murtala Mohammed.

A Talatar da ta gabata lauya Jimoh ya wakilici ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau na APC inda suka samu nasara a kan ɓangaren Gwamna Abdullahi Ganduje.

Lauyan Shakarau ya tabbatar wa jaridar Daily Nigerian da batun garƙame ofishin nasa, yana mai cewa shi da ma’aikatansa da sauran jama’ar da ke ginin lamarin ya shafa.

“Maganar da nake yi, yanzu haka ina cikin ginin ne tare da da jama’a da dama da aka garƙame mu tare. Ba mu ma san yadda za a yi mu fita ba”, in ji lauyan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *