Da Ɗumi-ɗuminsa: An ceto ma’aikatan Jami’ar Abuja

Daga BASHIR ISAH

Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja, ta tabbatar da cewa rundunar tsaron haɗin gwiwa sun ceto dukkan ma’aikatan Jami’ar Abuja da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Litinin da ta gabata.

Mai magana da yawun ‘yan sandan yankin, Josephine Adeh, ita ce ta bada wannan tabbaci cikin sanarwar da ta fitar a yau Juma’a.

Haka nan, Adeh ta ce tuni an sadar da waɗanda lamarin ya shafa da iyalansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *