Da ɗumi-ɗuminsa: An fatattaki ’yan bindiga cikin dare a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wasu ’yan bindiga da yawansu sun kai hari unguwar Sabon Tasha, ƙaramar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna cikin daren Asabar, 11 ga watan Disamba, 2021.

Rahotanni sun nuna cewa, ’yan bindigar sun banka wa gidan wani mutumi wuta bayan ƙoƙarin garkuwa da shi.

Jami’an Sojojin Nijeriya sun samu nasarar fatattakarsu bayan kirar da wani ya yi musu.

An tattaro cewa, Sojoji da ’yan bindigar sun yi musayar wuta da daddaren.

Wani shaidar gani da ido, Benjamin, ya bayyana wa manema labarai cewa, “’yan bindiga na ƙoƙarin shiga gida-gida kwashe mutane lokacin da sojoji suka isa. Mun gode wa Allah sojojin sun isa da wuri, da abin ya yi muni saboda sun shiga sace mai gidan ne amma babu kowa a gidan, sai suka banka wa gidan wuta cikin fushi”.

Manema labarai sun tattaro cewa, sai da aka kwashe awa guda ana musayar wuta tsakanin ’yan bindigar da sojoji.