Da Ɗumi-ɗuminsa: ‘Yan bindiga sun kashe sojan da suka yi garkuwa da shi daga NDA a Kaduna

An gano sojan Nijeriya da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi a safiyar Talatar da ta gabata a NDA Kaduna, amma a mace.

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Major Christopher Dator ne yayin harin da suka kai makarantar horar da manyan jami’an sojoji (NDA) da ke Kaduna ran Talata.

A cewar mai magana da yawun NDA, Major Bashir Muhd Jajira, jim kaɗan bayan aukuwar harin an tayar da rundunar jami’an tsaro ta musamman don su bi sawun ‘yan bindigar da zummar kuɓutar da jami’in da aka sace.

Tun farko, bayanai sun nuna ɓarayin sun buƙaci a biya su Naira miliyan 200 kafin su sako marigayin, amma sa’o’i kaɗan bayan da ‘yan bindigar suka buƙaci a biya su fansa sai aka gano gawar Major Christopher Dator cikin daren Talata.