Da ɗumi-ɗuminsa: An miƙa wa mai martaba Sarkin Kano Sanda

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Ana ci gaba da bikin miƙa sandar girma wanda Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bai wa Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da kuma ƙaddamar masa da ma’aikatan fadarsa.

Ana gudanar da wannan gagarumin taro ne yanzu haka a filin wasa na Sani Abacha da ke Unguwar Ƙofar Mata da ke ƙaramar hukumar Birnin Kano.

A wata sanarwa da Madakin Kano, Alhaji Nabahani Ibrahim, ya fitar ta ce an fara bikin ne tun ranar Alhamis ɗin da ta gabata, kuma ana sa ran kammalawa da hawan kilisa a jibi Litinin.

Kazalika, ko a jiya an gudanar da addu’a kuma za a gudanar da wasu addu’o’i na musamman a Babban Masallaci na Kano game da tsaro da kuma zaman lafiya.

Bikin dai ya samu halartar manyan sarakunan jihohin Najeriya da dama da baƙi daga ƙasashe daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *