Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano
Kungiyar Marubuta ta Ƙasa reshen jihar Kano, wato Association of Nigeria Author’s (ANA) ta zaɓi sabbin shugabanni. Zaɓen ya gudana ne a ɗakin karatu na murtala Muhammad da ke kan Titin Ahmadu Bello da ke Kano.
Dr. Maryam Ali Ali ce ta Jagoranci gudanar da zaɓen, waɗanda aka zaɓa sun hada da: Tjjani Muhammad Musa a matsayin shugaba, sai mataimakiyarsa Maimuna Idris Beli, da Mazhun Idris Ya’u a matsayin sakatare.
Haka kuma an zaɓi Danladi Z. Haruna a matsayin Ma’aji da sakataren kuɗi Abdullahi Lawan Kangala. Sai jam’in walwala Hausa, da Abdullahi Muhammad a matsayin Jami’in Hulɗa da Jama’a ɓangaren Turanci, da jami’ar walwala ind aka zaɓi Umma Sulaiman ‘Yan’awaki.
Kazalika, an zaɓi Hassan Ibrahim Gama a matsayin mai bada shawara a kan Shari’a, sai mai binciken kuɗi Bilkisu Yusuf Ali da sauransu.
A tara don samu cikakken rahoto a bugun Manhaja ta ranar Juma’a mai zuwa.