Da ɗumi-ɗuminsa: Buhari ya maida kakin soja

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya maida kakin soja albarkacin bikin faretin nuna ƙawa na Sojojin Nijeriya na 2023.

Buhari ya isa filin taron, Eagle Square – Abuja, sanye da kakin soja da misalin ƙarfe 10:18 na hantsi.

Bikin gabatar da launuka, biki ne da ke nuna ranar tunawa ko abin da ya faru a tarihin wata runduna ta musamman.

Daga cikin waɗanda suka mara wa Buharin baya har da Shugaban Fadar Ma’aikata na Fadar Shugaban Ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari, inda shi ma aka gan shi sanye da kakin na soja.

Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor, Babban Hafsan Sojoji, Lt.-Gen. Faruk Yahaya da kuma Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Usman Baba, na daga cikin malarta taron.