Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, zai kai ziyara Jihar Kano a gobe Alhamis, 16 ga watan Yuni, 2022.
Hakan na cikin saƙon da mai taimaka wa Shugaban Ƙasar kan sabbin kafafen sadarwa, Malam Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a yau Laraba.
Bashir Ahmad ya ce, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai je Jihar Kano ne domin halartar taron bikin yaye sabbabbin jami’an ‘yan sanda a Kwalejin Horas da ‘Yan Sandan da ke garin Wudil a jihar.