Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Babbar Kotun Jihar Kano mai Lamba 4 dake zaman ta a kan titin Mila, ta tabbatar da dakatarwar da wasu shugabannin Jam’iyyar APC a Mazaɓar Ganduje suka yi wa Shugaban Jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje daga jam’iyyar.
Alƙalin Kotun, Justice Usman Malam Na’abba ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata takardar da masu ƙara suka nema, ba tare da sanar wa ɓangaren waɗanda suke ƙara ba wato (Motion Ex parte).
Haladu Gwanjo da Laminu Sani ne suka shigar da ƙarar, inda suka yi ƙarar ɓangarori huɗu waɗanda suka haɗar da Jam’iyyar APC, Kwamitin Ayyukan Jam’iyyar na Ƙasa, Kwamitin zartarwa na Jam’iyyar APC na Jihar Kano da kuma Dokta Abdullahi Umar Ganduje.
Masu ƙarar dai sun shigar da roƙon su ta cikin wata takardar mai sakin layi Goma sha uku, tare da adireshin mai ƙara na biyu a ranar 16 ga watan nan da muke ciki, bisa Jagorancin Lauyan su Barista I. A. Sa’ad.
Takardar Umarnin ta amince waɗanda ake ƙara na farko da na biyu da kuma na huɗu, su maida martani ta wajen hurumin kotun, wato a ofis mai Lamba 40 dake kan titin Biantyre Crescent a Babban birnin Tarayya Abuja.
Ƙarain bayani na tafe