
Daga BASHIR ISAH
Shugaban Ƙungiyar Likitocin Nijeriya (NARD) Uyilawa Okhuaihesuyu, ya bada sanarwar janye yajin aikin sai baba ta gani da suka shiga.
Likitocin sun tsunduma yajin aikin ne tun a ranar 1 ga Afrilun da ya gabata.
Matakin shiga yajin aikin da likitocin suka ɗauka ya jefa asibitocin ƙasar nan cikin mawuyacin hali, lamarin da ya haifar wa marasa lafiya cikas na rashin samun kulawar da ta dace a asibitocin.
Kodayake dai likitocin sun janye yajin aikin ne bisa sharaɗin cewa idan Gwamnantin Tarayya ta gagara biya musu buƙatunsu, to fa za su koma su ci gaba daga inda suka tsaya.