Da ɗumi-ɗuminsa: Masu neman shugabancin APC sun janye wa Abdullahi Adamu

Ana gab da soma kaɗa ƙuri’a ne shida daga cikin ‘yan takarar shugabancin jam’iyyar APC da suka shirya fafatawa da zaɓin Shugaba Muhammadu Buhari, suka miƙa wuya suka janye takararsu.

Da wannan, ya tabbata cewa Sanata Abdullahi Adamu da ya kasance zaɓin Shugaba Buhari, shi ne zai zama shugaban jam’iyyar APC na ƙasa na gaba.

Wasiƙar da ta nuna janyewar ‘yan takarar

Wata wasiƙa da ta sami sa hannun Sanata Geoge Akume, a madadin ‘yan takarar ta nuna yadda baki ɗaya ‘yan takarar suka yi wa zaɓin Buhari mubaya’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *