Da ɗumi-ɗuminsa: Muhammad Abacha ya lashe zaɓen fidda gwani na takarar gwamnan Jam’iyyar PDP a Kano

Daga AMINA YUSUF ALI

Muhammad Abacha ɗa a gurin marigayi Sani Abacha, tsohon shugaban ƙasar Nijeriya na mulkin soja ya samu nasarar lashe zaɓen fid ga gwani na Gwamnan Kano a jam’iyyarsa ta PDP.

Jami’ar sanar da sakamakon zaɓen, Barista Amina Garba, ita ta bayyana Muhamad Abacha a matsayin wanda ya yi nasara bayan ya samu ƙuri’u 736 ya kayar da ɗan takarar da yake bin bayansa a yawan ƙuri’u, Jafar Sani Bello, wanda shi kuma ya samu ƙuri’u 710.

Shugaban kwamitin zaɓe, Mohammed Jamu, ya bayyana cewa, an gudanar da zaɓen bisa bin dokoki sannan an yi zaɓen tare da halastattun zavavvun daliget sannan hukumar zaɓen ta INEC da jami’an ‘yansanda da jami’an tsaro na ciki su ne suka kula da zaɓen.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa, ma’aikatan INEC guda shida ne suka je sanya ido a kan zaɓen; Mataimakiyar daraktan kula da zaɓe, Hauwa Hassan; Sakataren gudanarwa na ƙasa, Garba Lawal; Shugaban sashen Shari’a, Suleiman Alkali; Shugaban aiwatar da zaɓe, Sule Yaro; Shugaban sashen samar da katin zaɓe, Ocheka Edwin; da kuma shugaban sashen kuɗi da gudanarwa, Hassan Dalhatu.

A yayin da ake gudanar da wannan zaɓe na fid da gwani a nan jahar Kano wanda ya fitar da Muhammad Abacha a matsayin ɗan takarar gwamna a Kano wanda aka gudanar a shalkwatar jam’iyyar dake Lugard Avenue a Kano, a lokaci guda kuma ana gudanar da wani zaɓen fidda da gwanin na wani tsagin a jam’iyyar a wajen taro na Sani a dai birnin na Kano.

Majiyarmu ta bayyana cewa, sai dai har yanzu ɗaya tsagin ba su bayyana sakamakon zaɓensu ba, wanda aka ce har yanzu ba a kammala zaɓen ba.

‘Yan takarar wancan tsagin su ne, Yunusa Dangwani, Yusuf Dambatta, Mu’az Magaji Ɗan Sarauniya, Ibrahim Ali-Amin, Sadiƙ Wali da Mustapha Getso.