Da Ɗumi-ɗuminsa: Yau Buhari zai dawo daga London

A wannan Juma’ar ake sa ran dawowar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari daga London.

Buhari zai iso Nijeriya ne can da misalin ƙarfe 5 na yamma bayan shafe kwanaki kimanin 18 a Ƙasar Birtaniya.

Buhari ya halarci wani babban taro na duniya da aka shirya a kan sha’anin ilimi, wato GES a taƙaice, sannan bayan kammalawa ya tsaya duba lafiyarsa.

Buhari da Tinubu a London

A jiya Alhamis, an ga Buhari tare da jigo a jami’yyar APC, Bola Ahmed Tinubu awani hoto da aka yaɗa wanda ke nuni da lokacin da Buhari ya ziyarci Tinubu a London.