Da Ɗumi-ɗumu: An kama Manajan Darakta na Kano Line bisa zargin tada rikici a rumfar zaɓe

Daga RABIU SANUSI a Kano

Jami’an tsaro a Jihar Kano sun damƙe Manajan Darakta na kamfanin sufuri na jihar, Kano Line, wato Bashir Nasiru Aliko Koki, a mazaɓar Masaƙa dake Ƙofar Mazugal a birnin Kano.

Ana zarginsa ne da tayar da tarzoma tare da jagorantar ‘yan daba.

Ya zuwa haɗa wannan labarin an miƙa Bashir Nasirshi ga ‘yan sanda tare da wasu yaransa uku, sannan mutum sama da 200 sun arce.