Da ɗuminsa: Za a tuna da Buhari a matsayin Shugaban Ƙasa mafi inganci, inji Sarkin Lafia

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

An bayyana cewa, za a tuba da Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban Ƙasa mafi inganci a tarihin Nijeriya.

Wannan furuci ta fito ne daga bakin Mai Martaba Sarkin Lafia, Alhaji Sidi Mohammad, wanda kuma shine Shugaban Kwamitin Bada Lambobin Girma na 2022 da aka gudanar a yau.

Sarkin ya bayyana hakan a lokacin da ya ke gabatar da jawabin godiya a yayin bikin bayar da lambobin girmamawar, wanda aka gudanar yau a Ɗakin Taro na Ƙasa da ƙasa da ke Abuja.

A ta bakinsa, “bisa la’akari da irin fafutuka da gudunmawar da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ke bayarwa, don gina Nijeriya a matsayinsa na Shugaban Ƙasa, tarihi zai tuna da shi a matsayin Shugaban Nijeriya mafi inganci da aka taɓa yi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *