Daga BASHIR ISAH
Ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar PDP a Jihar Abia, Farfesa Uchenna Ikonne, ya riga mu gidan gaskiya.
Wannan na zuwa ne yayin da ya rage ƙasa da wata biyu kafin zaɓen 2023.
Babban ɗan marigayin, Chikezie Uche-Ikonne ne ya tabbatar da rasuwar marigayin a ranar Laraba.
“Cikin alhini nake sanar da rasuwar mahaifina, Farfesa Eleazar Uchenna Ikonne, wanda ya rasu a Babban Asibitin Ƙasa da ke Abuja,” in ji Uche-Ikonne.
Sanarwar ta nuna ɗan takarar ya rasu ne da misalin ƙarfe 4:00 na asuba bayan fama da taƙaitaccen rashin lafiya.
Ta ƙara da cewa nan gaba za a yi wa jama’a cikakken bayani bayan ahalin marigayin sun haxu sun tattauna.