Da ɗumi-ɗumi: APC ta haramta wa Malami da takwarorinsa kaɗa ƙuri’a yayin babban taronta

Daga BASHIR ISAH

Kwamitin riƙo da shirya babban taro na jam’iyyar APC (CECPC) ya haramta wa masu riƙe da muƙaman siyasa yin zaɓe yayin babban taron jam’iyyar da zai gudana gobe Asabar.

Cikin wani bayani da ya fitar a jiya Alhamis, kwmitin ya nuna cewa, “ɗaukacin masu riƙe da muƙaman siyasa waɗanda aka zaɓa a matsayin dalaget ga babban taron jam’iyya da zai gudana a ranar 26/3/2022 ba za su kaɗa ƙuri’a ba saboda dambarwar da ke tattare da sashe na 84 (12) na Dokar Zaɓe na 2022.”

Amma duk da wannan matsayar da aka cimma, kwamitin ya ce waɗanda lamarin ya shafa suna da damar zuwa wajen taron a matsayin masu sanya ido kawai.

Wannan ya biyo bayan ƙin amincewar da Majalisar Tarayya ta yi ne da Dokar Zaɓen da aka yi wa gyara wadda Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba wa hannu.

Bayanai sun nuna a Larabar da ta gabata Shugaba Buhari tare da gwamnonin APC suka haɗu suka yi ittifaƙi kan batun waɗanda suka dace su zama shugabannin jam’iyyar tasu a matakin ƙasa.