Da Ɗumi-ɗumi: Buhari ya tsige shugaban hukumar NDDC

Daga BASHIR ISAH

A ranar Alhamis Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tsige shugaban Hukumar Bunƙasa Yankin Neja Delta (NDDC), Effiong Akwa.

Sanarwar da ta fito daga hannun mai magana da yawun Ma’aikatar Kula da Harkokin Yankin Neja Delta, Patricia Deworitshe, ta ce, tsige Akwa da Buhari ya yi ya soma aiki ne daga ranar 20 ga Oktoba.

Sanarwar ta kara da cewa, an nada Mr Akwa shugaban NDDC ne na wucin-gadi na wa’adin lokacin da za a kammala binciken harkokin hukumar, don haka kammala binciken na nuni riƙon da aka bai Akwa ya zo ƙarshe kenan.

A cewar sanarwar, “Shugaba Buhari ya amince da kafa sabon kwamitin gudanarwa na hukumar daidai da tanadin Sashe na 5(2) na Dokar NDDC na 2000.”

Ma’aikatar Kula da Harkokin Yankin Neja Delta ita ce mai haƙƙin kula da hukumar NDDC.