A ranar Laraba, mayaƙan Boko Haram/ISWAP su 314 suka miƙa wuya ga sojojin da ke yaƙi da ta’addanci a yankin Ƙaramar Hukumar Bama da ke Jihar Borno a shiyyar Arewa maso gabashin Nijeriya.
Babban Ofishin Sojiji ne ya bayyana hakan a shafinsa na facebook.