Da ɗumi-ɗumi: Yadda ake fafatawa a zaɓen gwamnan Anambara na 2021

  • An yi gyara a tsarin tsaro
  • Ba za a yi zaɓe ba a rumfunan zaɓe 86, inji INEC
  • Ɗan takaran jam’iyyar AAC, Chidozie Nwankwo ya janye daga takarar zaɓen gwamnan Anambara
  • Na’urar BVAS ta mazaɓar Soludo ta ƙi aiki
  • Masu kaɗa ƙuri’a sun ɓalle da zanga-zanga kan dokar INEC ta hana marasa takunkumi zaɓe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Da misalin ƙarfe 8:30 na safiyar yau Asabar ne aka fara kaɗa ƙuri’a a rumfar zaɓen PU005, Umudioka, ƙaramar hukumar Dunukofia da rumfar zaɓe ta Area 13, Ichida 1, ƙaramar hukumar Anaocha ta Jihar Anambara.

Kamar yadda muka sani ne cewa, ’yan takara 18 ne suke fatan maye gurbin Gwamna Willie Obiano. Waɗanda daga cikinsu akwai:

Charles Soludo – APGA

Senator Andy Uba – APC

Valentine Ozigbo- PDP

Sanata Ifeanyi Ubah – YPP

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa, akwai akwatuna 1,820 da za su karɓi masu kaɗa ƙuri’a 846,994 a mazaɓar Anambara ta arewa.

A mazaɓar Anambara ta tsakiya, za a samu akwatunan zaɓe 3,987 waɗanda za su karɓa masu kaɗa ƙuri’a 887,295 da suka yi rijista.

A Anambara ta kudu, za a samu akwatunan zaɓe 1,934 domin masu kaɗa ƙuri’a 794,203. Jimillar masu kaɗa ƙuri’ar da suka yi rijista sun kama 2.52 miliyan.

Su ne za su fitar da makomar ɗan takarar da zai shugabanci Jihar a shekaru huɗu masu zuwa.

An yi gyara a tsarin tsaro:

Sufeto Janar na ’yan sandan, IGP Alkali Usman Baba ya cire mataimakin Sufeto Janar na ’yan sandan, DIG Joseph Egbunike a matsayin shugaban tawagar tsaro na zaɓen gwamnan Anambara ’yan sa’o’i kaɗa kafin zaɓen.

Kakakin rundunar ’yan sandan ƙasar, CP Frank Mba, ya tabbatar da cewar an sauya wa DIG Egbuike wurin aiki, amma bai bayyana dalilin cire babban jami’in wanda ya kasance ɗan asalin Jihar Anambara ba.

Ba za a yi zabe ba a rumfunan zabe 86, in ji INEC:

Yayin da ’yan Anambara ke shirin zaɓe, a lura cewa hukumar INEC ta bayyana a baya cewa ba za a yi zaɓe ba a rumfuna 86 cikin rumfunar zaɓe 5,720 da ke Jihar saboda ba su da masu jefa ƙuri’u.

Ɗan takaran jam’iyyar AAC, Chidozie Nwankwo ya janye daga takarar zaben gwamnan Anambara:

Ɗan takara jam’iyyar ‘African Action Congress’ AAC, Chidozie Nwankwo, ya janye daga takarar kujeran gwamnan Jihar Anambara.

Nwankwo ya sanar da cewa dukkan waɗanda suka yi niyyar zaɓensa yanzu kawai su goyi bayan ɗan takarar jam’iyyar PDP, Valentine Ozigbo.

Na’urar BVAS ta mazaɓar Soludo ta ƙi aiki:

Masu kaɗa ƙuri’a sun fusata. Kamar yadda suka ce, na’urar BVAS ta ƙi aiki a mazaɓar ɗan takarar Charles Soludo.

Masu kaɗa ƙuri’a sun ɓalle da zanga-zanga kan dokar INEC ta hana marasa takunkumi zaɓe:

Masu kaɗa ƙuri’a a gunduma ta 9 da ke Ezimezi a Amawbia, ƙaramar hukumar Awka ta kudu, sun ɓalle da zanga-zanga kan dokar INEC ta hana marasa takunkumin fuska saka jefa ƙuri’a.
Masu zaɓen sun dinga tururuwar fitowa tun wurin ƙarfe 8:30 amma sai aka ce su koma gida tare da sako takunkumin fuska.

Wannan lamarin ne yasa tsohon ɗan majalisar Jihar Anambra, Chikodi Aghanya ya kwatanta lamarin da ‘shirme’.

Jaridar Manhaja za ta cigaba da kawo muku bayanai kan yadda zaɓen ke tafiya. Ku kasance tare da mu…