Da alama ba a ankara ba a Anka

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Duk lamarin da mutum ya ankara ya iya taɓuka wani abu da yardar Allah don kar a yi masa sakiyar da ba ruwa. Ankara na taimaka wa mutum ya samu ya shirya tsaf don tunkarar abin da zai fuskanto shi. Don muhimmancin ankara ake son mutum mai shirin tafiya ya tsara komai kan lokaci don kar ya kai ga fafa gora ranar tafiyar.

Fafa gora ranar tafiya kan sa a sha ruwan guzuri da aka zuba a gorar ya zama mai ɗaci don gorar ba ta bushe ba ko ba a ba da tazarar da za a iya aiki da ita ba. Yana daga muhimman lamura a rayuwa mutum ya samu labarin lamari kafin ranar bayyanarsa.

Samun labari na da wani ginshiƙin aikin gwamnati ko jami’an tsaro ko ma ‘yan siyasa. Idan ka na da labarin halin da abokin hamayya ke ciki za ka iya ƙunce masa ɗamarar yaƙi ba tare da jiran har sai ya yi ma ka illa ba. Duk masu karanta labarun yaƙi da ya haɗa da na zamanin zamuna zai ji ana tura wasu masu leƙen asiri da kan samo labarin halin da abokan gaba ke ciki da hakan zai taimaka a san shirin da za a yi mu su don samun nasara a kansu.

Masu leƙen asiri kan gano shin dakaru nawa ne a rundunar abokin gaba, dawaki nawa ne, takubba, kibau da sauransu guda nawa ne. Haka nan za a iya ganowa maza nawa ne kuma mata nawa ne. In an ƙara matsa lamba za a gano dakarun ƙwararru ne ko ’yan dagaji ne ko ma akwai sojojin haya a cikinsu. Shin duk sun miƙa wuya ga kwamandan su ko akwai rabuwar kawuna?

Haƙiƙa duk inda aka tattara irin waɗannan muhimman bayanan za a san matakan ɗauka na ci gaba da tunkarar abokan gaba ko sake sabon shiri ko ma in abin ya yi muni a nemi sulhu da miƙa wuya. A zamanin yau akwai hanyoyin kimiyya da fasaha da a kan samu labarun asiran abokan gaba. Duk da kimiyyar ta binciko bayanai ko ma kutsawa na’urori don satar bayanai, bai hana kuma aikin wasu hukumomin sirri da ke da jami’an da kan shiga fagen ‘yan hamayya ko gaba don sanin halin da su ke ciki.

Yawancin ƙasashen duniya da suka cigaba na da sanannun hukumomin leƙen asiri da kan shiga lungu-lungu da saƙo-saƙo na duniya don samo bayanai. Gwamnatoci kan kashe maƙudan kuɗi don ɗaukar nauyin irin wannan bincike saboda aikin bayanan da a ke ganowa na dawo da sakamako da ya fi kuɗin da ake kashewar riba. Bayanan kan sa ƙasa ta kare mutuncinta da ’yancinta a tsakanin sauran ƙasashe.

Baya ga irin waɗannan hukumomi da kan samo bayanai musamman daga ƙetare don amfanin ƙasa akwai kuma hukumomin da kan tattara bayanan daga cikin gida don gano ƙulle-ƙullen miyagun iri na kawo barazana ga zaman lafiyar sauran jama’ar kirki na ƙasa. A wannan aiki a kan samu jami’an da kan zama mahaukata na gangan su zauna a wasu sassan ƙasa don farautar labaru kuma ranar da suka samu labarin sai su ɓace su koma wani sashen ƙasa don komawa masu hankali ko sake aiki a matsayin mahaukatan. A kan samu masu goge takalma ko yankan farce ma a cikin jami’an da kan shiga cikin jama’a sun a tara bayanan sirri don amfanin haɗin kai da tsaron ƙasa.

Shin me yake faruwa ne a garuruwa da ƙauyukanmu musamman Arewa maso yamma har ta kai ga an mamayi mutane a ƙauyensu a kashe su ba tare da ankarar jami’an tsaro ba? Me ke faruwa a Arewa maso gabas da ’yan ta’adda kan mamayi cibiyoyin jami’an tsaro har su yi varna ba tare da ɗaukar matakin kariya ba bisa bayanan sirri? A makon nan dai an samu labarin yadda ’yan bindiga suka shiga ƙauyuka na ƙaramar hukumar Anka a jihar Zamfara suka kashe mutane da ƙona shaguna. Zubar da jinin ya yi muni kuma ya shafi mutanen gari ne da ba su ankara ba.

Ɗaya daga cikin mazauna ƙauyukan ƙaramar hukumar Anka a jihar Zamfara, Murtala Waramu ya ce, shi da sauran jama’a sun ƙirga gawarwaki 52 da ’yan bindiga suka yi wa kisan gilla a wani mummunan farmaki da su ka kawo. Murtala wanda yake cikin masu gudun hijira a Anka ya ce, har yanzu suna ta binciken sauran mutane da ba a gani ba don sanin ko su na raye ko kuwa a’a.

Murtala ya ƙara da cewa, da sun samu ƙwarin gwiwa daga jami’an tsaro ta hanyar kasancewa tare da su ko dafa musu baya, za su iya fatattakar ɓarayin da amfani da bindigarsu ta harbi-ka-ruga.

A yanzu dai a cewar Murtala, mutane sun samu an buɗe mu su makarantun firamare a garin Anka inda su ke samun mafaka. Masu hijirar sun haɗa da maza da mata. Da alamun ƙurar harin ta lafa don ‘yan bindigar sun wuce cikin ƙungurmin daji bayan sace dabbobin gida da jama’ar ƙauyukan ke kiwo.

Rahotanni daga masu gudun hijira a garin na Anka sun bayyana cewa an gudanar jana’izar waɗanda suka rasa ransu a sanadiyyar harin ’yan bindiga a kimanin ƙauyuka biyar. An ba da labarin tattaro wasu gawarwaki daga dazuka da yi musu sutura a manyan ramuka.

Wani jami’in gwamnatin jihar Zamfara ya bayyana cewa, an samu akasin harin ne yayin da ‘yan bindiga ke ƙaurace wa yankunan jihar Sakkwato suna shiga Zamfara don farmaki da jami’an tsaro ke kai musu. Majiyoyin tsaro na nuna ’yan bindigar na guduwa ne don samun maɓoya sanadiyyar ɓarin wuta da ake yi musu a Sokoto.

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawallen Maradun ya kai ziyara ƙaramar hukumar Anka da Bukkuyum don duba halin da jama’a ke ciki biyo bayan harin ‘yan bindiga. Ko ma dai ba wani tasiri, ziyarar na da ma’ana don mutan ƙauyuka za su ji a jikinsu cewa gwamnati ta san da zaman ko da ba ta da kyallen share musu hawaye.

An samu labarin gwamnan ya gana da jagororin sassan tsaro don samun ƙarin bayani kan wannan hari don ɗaukar matakai. Hakan ya nuna za a jira a ga sakamakon sabbin matakai da suka saɓa da na baya da hakan ya haca da rufe layukan sadarwar wayar salula da daina neman sulhu da miyagun irin.

Yanzu haka akwai ‘yan gudun hijira a manyan garuruwan ƙananan hukuomin biyu da ke samun kayan tallafi. An ruwaito kwamishiniyar jinƙai ta jihar Hajiya Fa’ika Ahmad na bayyana tura kayan agajin.

Hare-haren ’yan bindiga ya zama ruwan dare a wasu jihohin Arewa maso yamma da Neja a Arewa ta tsakiya. A zantawa da shi ta musamman da gidan talabijin na Channels, shugaban Nijeriya Muhammdu Buhari ya ayyana ɓarayin daji da ’yan ta’adda.

Hakan ya biyo bayan yanke matsayar ce da kotu ta yi da kuma goyon bayan hakan daga ‘yan majalisar dokoki. Sai dai hanzari ba gudu ba, shin zaman ‘yan Boko Haram ‘yan ta’dda ko zaiyana su da cewa ‘yan ta’adda ne ya sa an iya murƙushe su gaba ɗaya a tsawon shekaru kimain 12 da ake tafka yaƙi da su?

A fili dai ya nuna ɗaukar matakai na haƙiƙa na dawo da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a ke buƙata. A gaskiya ba irin gawar da ba a gani da ta haɗa da ta farar hula mutan gari, ta jami’an tsaro da ma su kan su ’yan ta’addan. Baya ga buɗe wuta ko shata daga tsakanin jami’an tsaron gwamnati da miyagun iri, yana da kyau a tono tarihin yadda aka fara sassan Nijeriya suka shiga wannan mummunar fitina.

Gano dalilan zai sa a san yasda za a magance matsalar gaba ɗaya. Kamar mutum ne ya zo gidansa ya ga ya malale da ruwa daga wani fonfo. Matakin farko da ya dace ya ɗauka shi ne ya rufe ko ya kashe fonfon. Kullum a kan so komawa tushe ne zai maganin lamari. Sare rassan bishiya ba ya nuna jijiyoyin ta da ke can cikin ƙasa sun mutu. Hakanan in an kashe mugun maciji sai an sare kansa kamar a yi ajiyar zuciya cewa komai ya wuce mutane za su iya yin barci da ido biyu rufe don dafi ya gushe.

Gaskiya ne lamarin dawo da tsaro a irin wannan yanayi sai ya haɗa da taimakon kowa.