Da amincewar ma’aurata na ɗaura masu aure duk da ɗayansu na ɗauke da cutar HIV – Korarren Hakimi

Daga UMAR GARBA a Katsina

Jama’a na ci gaba da ce-ce-ku-ce kan dakatar da basaraken gargajiya a Katsina da gwamnatin jihar ta yi, saboda zarginsa da gwamnatin ta yi na ɗaura auren wasu ma’aurata biyu inda ɗaya daga cikinsu na ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki.

Gwamnatin jihar ta ce binciken da ta yi kan lamarin ta gano Alhaji Abubakar Abdullahi Ahmadu (Sarkin Kurayen Katsina), Hakimin gundumar Kuraye, ya karya dokar yin gwaji tsakanin wasu masu niyyar yin aure lamarin da ya sa gwamnatin ta tuɓe masa rawani.

Sai dai basaraken ya bayyana wa manema labarai cewar da amincewar ma’auratan ya jagorancin ɗaurin auren inda dukkansu sun san matsayin juna tun da farko.

Hakimin ya ce duk da matar ƙanwarsa ce, sun bi dokar da gwamnatin ta kafa na yin gwaji, kuma bisa amincewar ma’auratan da kuma shawarar likitan dake duba lafiyar matar aka ɗaura auren.

“Mun bi dokar yin gwaji kafin ɗaura auren saboda, mijin yasan matsayin matar, amma ya ce ya ji ya gani.

“Ba mu ɗaura auren ba sai da muka tura matar wajen likinta dake ba ta magani, mijin shi ya ce yana son matar ba tilasta masa aka yi ba, sai da matar ta gaya ma sa muma muka gaya masa.” Inji Basaraken.

Idan za a iya tunawa, Manhaja ta kawo lamarin yadda gwamnatin jihar Katsina, ta sauke Alhaji Abubakar Abdullahi Ahmadu daga sarautar sa ta Sarkin Kurayen Katsina cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na sakataren gwamnatin jihar ya fitar.

Sanarwar ta bayyana cewar, an cire basaraken ne bisa laifin ɗaura auren wasu ma’aurata biyu mata da miji ba tare da takardar gwajin lafiya ba daga likita. Matakin ya savawa doka kamar yadda sanarwar da Abdullahi Aliyu ‘Yar’adua ya saka wa hannun ta bayyana.

Ita ma masarautar Katsina ta fitar da irin wannan sanarwa, ta hannun sakataren masarautar cewa, an cire sarkin ne bisa jagorantar ɗaura auren Alh. Lawal Mamman Auta da Hajiya Halimatu Abdullahi Kuraye inda ɗaya daga cikinsu na ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Basaraken ya ce shekarar sa 16 yana mulkin masarautar ba tare da samunsa da aikata wani laifi ba, sai dai wasu daga cikin al’umar jihar na ganin ana son a naɗa wani na hannun damar gwamnan jihar ne shiyasa aka tuɓe ma sa rawani.