Da babu gara babu daɗi

Daga IBRAHIM YAYA

A kwanakin baya ne, aka kawo ƙarshen babban taron ƙasashe masu ruwa da tsaki kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MƊD karo na 27 wato COP27 a wurin shakatawa na Sharm el Sheikh dake ƙasar Masar, wanda tun farko aka shirya kammala shi a ranar 18 ga wata, inda mahalarta taron suka zartas da ƙudurori da yawa, tare da yanke shawarar kafa wani asusu na musamman da zai tattara kuɗaɗen taimakawa ƙasashe masu tasowa da wadanda ke fama da matsalar sauyin yanayi.

Taron na bana, shi ne na 27 da ƙasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MƊD ko UNFCCC suka gudanar, kuma cikin wata sanarwa da ya fitar game da hakan, babban magatakardar MƊD, Antonio Guterres ya yi na’am da kafa asusun, wanda zai samar da diyyar asara da lalacewar muhalli, yana mai fatan asusun zai yi aiki yadda ya kamata.

Fata dai shi ne, a gani a ƙasa, wani ana biki a gidansu kare.

Taron na Sharm El-Sheikh na ƙasar Masar, ya zamo wani ginshiki mai muhimmanci na tabbatar da adalci.

Sai dai kuma a cewar Guterres, duk da cewa, kuɗaɗen da ake fatan tarawa ba za su isa ba, yunkurin tara kuɗaɗen kaɗai, tamkar tabbatar da aniyar siyasa ce da za ta sake gina amincin da ya riga ya gurgunce.

Idan ruwanka bai isa alwala ba, aka ce sai ka yi taimama.

Bugu da ƙari, taron na COP27 ya yi rawar gani, wajen zaƙulo matakan jure sauyin yanayi, da tattara kuɗaɗe na diyyar asara da lalacewar muhalli, waɗanda su ne manyan abubuwan damuwa ga ƙasashe masu tasowa.

Yayin taron na bana, ƙasashe masu wadata sun fito da muhimman batutuwa da suka dace, kamar batun samar da kuɗaɗen, da tallafin ƙwarewa da ƙasashe masu tasowa ka iya cin gajiyar su, suna fatan ƙasashe masu wadata za su yi aiki tare da sauran sassan ƙasa da ƙasa, wajen gina yanayi mai dorewa domin gobe.

Fata dai shi ne ƙasashe masu sukuni, za su ba da gudummawar da za ta kai ga cimma nasarar ƙudurin dake ƙunshe cikin yarjejeniyar Paris, ta hanyar kafa asusun diyyar asara da lalacewar muhalli, domin taimakawa ƙasashe masu tasowa, ta yadda za su shawo kan ƙalubalen sauyin yanayi.

Masu fashin baki na cewa, idan har mafarkin kafa wannan asusu ya tabbata tare da aiwatar da shi kamar yadda aka tsara, to, wata rana batun matsalar sauyin yanayi za ta kasance tarihi. Fata na gari dai aka ce lamiri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *