Daga BASHIR ISAH
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da korar manyan jami’an Hukumar Hajji a yankunan ƙananan hukumomi 44 da jihar ke da su tare da naɗa waɗanda za su maye gurbinsu wajen ci gaba da ayyukan Hajjin 2023 a faɗin jihar.
Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar a safiyar Lahadi mai ɗauke da sa-hannun Sakataren Yaɗa Labarai ga Gwamna, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ta nuna Gwamnan ya ba da umarnin jami’an riƙon da aka naɗa su karɓe ragamar ayyukan Hajji daga jami’an da aka kora.
Kazalika, sanarwar ta buƙaci waɗanda aka naɗan da su kai kansu ofishin sabon Darakta Janar na Hukumar Alhazan Jihar ranar Lahadi, 4 ga Yuni, 2023 a Hedikwatar Hukumar don taron gaggawa.
Majiyarmu ta tattaro cewar, naɗin jami’an riƙon wanda galibinsu ‘yan Kwankwasiyya ne, hakan ya biyo bayan korarrun jami’an sun kammala yi wa maniyyatan jihar rijista da kuma tattara dukkan bayanan maniyyatan ne.
Wannan sauyin na zuwa ne yayin da ya rage ƙasa da sa’a guda kafin fara jigilar maniyyatan Jihar Kano zuwa ƙasa mai tsarki.
Idan ba a manta ba, da fari Gwamna Kabir ya maye gurbin Ambasada Mohammad Abba Danbatta da Alh. Laminu Rabiu a matsayin Shugaban Hukumar Alhazai ta jihar.