Da Dumi-ɗumi: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban jami’a a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

A daren Alhamis da ta gabata wasu ‘yan bindiga suka yi dirar mikiya a yankin Sabon Gida a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da wasu ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau (FUGUS) waɗanda ba a kai ga tantace yawansu ba.

An ce ɗaliban da lamarin ya shafa na zama ne a wajen Jami’ar.

Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida ma wakilinmu ta waya cewar, maharan sun shiga wurin kwanan ɗalibai guda uku inda a nan suka kwashi ɗaliban.

“Yanzu da nake zancen nan da kai, maharan sun yi garkuwa da ɗalibai mata da dama, sai ‘yan kaɗan da suka samu suka tsere. Kuma babu wanda ya san adadin waɗanda aka kwashe,” in ji shi.

Sai dai ya zuwa haɗa wannan labari, lyan sanda yankin ba su ce komai a kan batun ba.