Da jarin Naira 50 na fara kasuwanci – Matashi Dini Majia

DAGA MUKHTAR YAKUBU a Kano

A wannan lokacin da ake ganin matasa suna da son su samu rayuwa cikin sauqi ba tare da sun tashi sun nemi na kansu ba. Don haka da yawa sai matasan suka zama marassa aikin yi da kuma dogon buri na yin rayuwa mai tsada. Sai dai ba a taru an zama ɗaya ba, domin kuwa Dini Muhammad Majia yaro ne matashi da tun farkon rayuwar sa ya taso da zuciyar neman na kansa, wanda a yanzu yana cikin matasan ‘yan kasuwa a cikin garin Kano, wanda kuma yake da kishin samar wa matasa hanyoyin kasuwanci da sana’o’in dogaro da kai. Wakilin Blueprint Manhaja, Mukhtar Yakubu ya tattauna da shi don jin yadda ya fara kasuwancin da kuma Irin abubuwan da ya fuskanta. Don haka, sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.

MANHAJA: Da farko za mu so ka gabatar da kanka da kuma harkokin kasuwancin da kake yi.

MAJIA: To Alhamdullahi, ni dai sunana Dini Muhammad Majia, an haife ni a Unguwar Tudun Murtala ta Ƙar amar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano, kuma ni matashi ne a yanzu ban fi shekara 30 zuwa da ɗaya ba.

Da yake kai ɗan kasuwa ne za mu so ka faɗa mana yadda ka fara kasuwancin naka.

To, ni dai asalin kasuwancina a gida na fara yin sa da sayar da rake. Idan mun dawo daga makaranta, sai na je na sayo rake. tun ina sayo na Naira 50, har ya kai da taimakon Allah da kuma goyon baya da Mahaifiyata take ba ni, har ya kai nake sayo dami ɗaya. Kuma daga nan da abin ya ci gaba, sai na fara harkar kanti, aka ci gaba da gurgurawa, daga nan sai na faɗa harkar kiwon dabbobi wanda na fara da akuya, kuma alhamdullah ya karve ni.

Sai kuma na koma harkar raguna duk Sallah, na sayar na haɗa kuɗina. Kuma daga nan sai na ci gaba in da ɗanuwan Mahaifiyata ya ɗauke ni ya tafi da ni Kasuwar Kantin Kwari na zama yaron rumfa. Aka ci gaba da tafiya a haka, muna harkar sayar da shadda har zuwa wani lokaci. Kuma duk da ina a matsayin yaro, to ni ma ina da kuɗina wanda na san a lokacin ina da kuɗi sama da Naira dubu ɗari sama da shekaru goma da suka wuce.

Kuma alhamdullah a wancan lokacin yaro kamar ni a wajen ba na jin akwai wanda yake da wannan kuɗin. Muna harkar, sai kuma maigidanmu ya koma harka da ‘yan Chana, da haka har Allah ya sa nima ‘yan Chana suka ba ni Shago ɗaya suka karɓe ni daga wajen maigidana, kuma ya ba ni dama na tafi muke harka da su, wanda a yanzu sai godiyar Allah, don har mun samar da wasu harkokin kasuwanci da muke yi namu na kanmu kamar, harkar biredi wanda ake yi a nan Unguwar Tudun Murtala mai suna Majia Bread, sannan ina yin harkar ruwa fiya wata.

Kuma gaskiya wannan harkar da nake yi, ba na kallon ribar da zan samu, ina kallon yadda zan samu na rage matasan da ba su da aikin yi a cikin al’umma. Kuma a gidan biredin ina da ‘yanuwa da matasa da yawa da suke cin abinci da samun abinda za su rufa wa kansu asiri da kuma iyayensu, kuma nakan duba dai-dai yanayin matasan, idan wanda ya kamata a kai shi kasuwa ne, sai a kai shi. Idan kuma wanda za a kai shi gidan Biredin ne, shikenan.

Saboda idan matashi yana karatu ka kai shi kasuwa to kasuwancin zai taɓa karatun, don haka sai dai a bar irin wannan a wajen aiki. Saboda mu dai mun gaji kasuwanci ne a wajen iyayenmu maza da mata, kuma muna samun ci gaba, saboda shawarar iyaye da kuma albarkarsu.

A matsayinka na matashin da ka zama babban ɗan kasuwa, ko ya kake ganin iri ƙalubalen da matasa suke fuskanta ta fuskar kasuwanci?

To, ni da yake ina da iyaye masu ba ni shawara, don haka ina bin abin cikin tsari tare da taka-tsan-tsan, don haka, ina samun lambar yabo. Don haka, ake ganin ina ƙaramin yaro amma na samu gogewa, kuma ba komai ba ne ya jawo haka, sai wajen da na taso da aka riƙe ni aka koya mini kasuwancin kuma su iyayen dai su suka koya mana haka. Sannan kuma da yin abota da mutane na ƙwarai, wannan ya sa kullum muke samun ci gaba. Don a yanzu haka, mutanen da suke ƙarƙashin kasuwancina matasa irina suna da yawan gaske. Kuma wannan ita ce Babbar nasara da na samu a rayuwa ta wato samar wa matasa hanyoyin dogaro da kansu.

A yanzu wanne burin ka sa a gaba a matsayinka na matashin ɗan kasuwa?

Ni a yanzu burin da nake da shi bai wuce neman Allah ya hore mini na samar da wata babbar ma’aikata da za ta ɗauki matasa masu yawa aiki. Ba domin komai ba, da yawa idan na ga sana’ar wasu daga cikin abokaina, sai na ga da ƙarfina ya kai, sai na taimaka musu, don muna da matasa masu yawa a cikin unguwanni da suke buƙatar hakan. Don haka, nake da wannan burin na samar wa da matasa aikin yi.

Daga ƙarshe wanne kira za ka yi ga matasa a game da riƙon da harkar kasuwanci?

To, ni kiran da zan yi ga matasa, da yake ina da wani vangare na harkar ƙwallon ƙafa, wato Majia Academy. Ina ganin matasa masu baiwa har nake kiran su na ba su shawara a kan su yi ƙoƙarin yin amfani da baiwar da Allah ya ba su, domin ba ta haɗuwa da abu biyu. Ko dai ka yi Bal ɗin, ko ka yi abin da ka ƙware da shi. Amma dai babban abin da matasa za su tsaya a kansa shi ne, neman ilimi da biyayya ga Iyaye da sauran manya da ake tare da su, kuma ina fatan matasa su yi siyasa cikin hankali da nutsuwa.

To madalla, Malam Dini, mun gode.


Ni ma na gode sosai.