Da kuɗi na maganin mutuwa da mun kashe ko nawa ne don kuɓutar da Sani Ɗangote – Tinubu

Daga BASHIR ISAH

Jagoran jam’iyyar APC na ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana rasuwar Marigayi Sani Dangote a matsayin al’amari da Allah Ya nuna ikonSa, yana mai cewa, da kuɗi na maganin mutuwa da sun haɗa ko nawa ne don kuɓutar da Sani daga hannun mutuwa.

Tinubu ya bayyana haka ne sa’ilin da ya ziyarci Alhaji Aminu Alhassan Dantata a Juma’ar da ta gabata dangane da rasuwar Sani Ɗangote.

Tinubu wanda ya kai ziyarar a bisa rakiyar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya ce da kuɗi na sayen rai da ko nawa ne za su kashe don tsawaita ran Marigayi Sani.

“Mutuwar Sani ta bayyana ƙarfin ikon Allah, ba wai batun kuɗi ba ne, inda a ce kuɗi na magani da za mu kashe ko nawa ne.

“Babu abin da wani mahaluki zai iya yi a kan haka. Amman wannan shi ne abin da Allah Ya so. Haka Allah Ya riga Ya rubuta babu wanda ke da ikon canjawa.

“Mun zo nan ne domin mu taya ku jimamin wannan rashi don ku sami sassaucin zafin rashin. Da fatan Allah Ya faranta maka Ya kuma ba ka ƙoshin lafiya. Allah Ya bai wa Sani Ɗangote Aljanna Firdaus.”

Daga bisani, Tinubu ya ziyarci attajirin da ya fi kowa kuɗi a yankin Afirka, Aliko Dangote a Kano wanda wa yake ga marigayin.

Bayan haka, Tinubu da Ganduje sun haɗu da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero inda suka gabatar da Sallar Juma’a tare.